Real Madrid na da ƙwarin-gwiwar saye Kylian Mbappe mai shekara 23, kuma za su yi duk mai yiwuwa domin mallakar ɗan wasan na PSG mai buga gaba a Faransa, bayan sun fahimci cewa ɗan wasan da suke hari, Erling Braut Haaland, zai tafi Manchester City. (Mail)
Real ta matsu ta mai do da ɗan wasan Ingila Jude Bellingham Bernabeu, amma Borussia Dortmund ba ta da niyyar sakin ɗan wasan mai shekara 18, kuma tana kokarin ƙara masa albashi don shawo kansa ya ci gaba da zama da su. (Bild – in German)
Everton na sa ido kan ɗan wasan Wolves’ Adama Traore, mai shekara 26, tana sa ran iya sayen ɗan wasan na Sifaniya idan Barcelona taƙi tabbatar da zamansa na dindindin a Nou Camp.(Football Insider)
Sabon kocin da Manchester United ke shirin karɓa Erik ten Hag na da damar kashe £200m wajen sayo sabbin ‘yan wasa, yayinda ‘yan wasan shidan farko a kungiyar ke shirin bankwana da ita a wannan kakar. (Mirror)
Anthony Martial mai yiwuwa ya kuma Old Trafford bayan zaman aro na tsawon lokaci a Sevilla, yayinda kungiyar ta Sifaniya ba ta nuna alamun ci gaba da zama da dan wasan na Faransa mai shekara 26. (Fabrizio Romano)
Wakilan Paul Pogba sun tattauna da Juventus da Real Madrid kan yiwuwar ya sauya sheka, idan kwantiragin matashin mai shekara 29 ya kare. (Sky Sports)
KocinTottenham Antonio Conte na shirin tattaunawa da Daniel Levy, zai shaidawa shugaban kungiyar cewa suna bukatar dauko sabbin ‘yan wasa shida, akwai ɗan wasan Leicester asalin Belgium Youri Tielemans, mai shekata 24, da ke kan gaba. (Telegraph – subscription required)